TSAFI KO MAGANI: TA{AITACCEN NAZARIN KANGIDA DA NAU’O’INSA A {ASAR KWATARKWASHI 

0
556
You can download this material now from our portal

TSAFI KO MAGANI: TA{AITACCEN NAZARIN KANGIDA DA NAU’O’INSA A {ASAR KWATARKWASHI 

BABI NA [AYA: Gabatarwa 1.0 Gabatarwa

Babban burin wannan nazarin shi ne na bin sawun ]aya daga cikin nau’o’in bautar gargajiya da Hausawa suke aiwatarwa. Wannan bautar ita ce, ta kan-gida. Don samun sau}in gudanar da nazarin an kasa aikin zuwa babuka biyar. Ga yadda aka shirya gudanar da binciken a kowane babi.

A babi na ]aya bayan shimfi]a sai aka gudanar da bitar ayyukan da masana da manazarta suka gudanar. Bayan an kammala nazartar ayyukan sai aka sami dalilin da ya haifar da gudanar da wannan nazarin, saboda ba a sami wani aiki da ya yi daidai da wannan nazarin ba ko da ta take ko farfajiyar da aka ke~e wa aikin. An kawo hanyoyin da aka bi don samun nasarar kammala binciken. An bayyana irin mahimmancin da binciken yake da shi bayan an kammala shi, daga nan sai aka na]e babin.

A babi na biyu kuwa bayan shimfi]a sai aka kawo tarihin samuwar garin Kwatarkwashi da kafuwarsa da ire-iren sana’o’in mutanen garin suke gudanar wa. Babin ya kawo bayani kan irin al’adun da mutanen Kwatarkwashi suke gudanarwa tare da yanayin }asar garin. A }ar}ashin yanayin }asar an dubi yanayinta da yanayin lokuta na shekara. An kawo yadda garin Kwatarkwashi ya samo asalin sunansa na Kwatarkwashi, tare da tsarin masarautarta. An bayyana sarakunan da suka mulki garin tun daga shekarar 1400 zuwa yau. An kawo yadda tsarin gidan sarautar garin Kwatarkwashi yake, inda aka bayyana akwai gida biyu a gidan sarautar. An na]e babin daga }arshe.

Babi na uku kuwa an yi fashin ba}in kalmomin tubalan binciken ne don samawa mai sha’awar karatu fahimtar inda aka dosa. A babi na hu]u an kawo dalilan da suka haddasa bautar gargajiya ga Hausawa, tare da bayyana yadda Bahaushe ke aiwatar da tsarin bautarsa a gargajiyance. Bayan nan sai aka koma kan mahimmin binciken inda aka bayyana ire-iren kangida a garin Kwatarkwashi, tare da mahimmancin. An yi bayanin matsayin kan gida a da, da yanzu. Sannan aka kawo yadda ake bautar kangida tare da jero ire-iren aljanun da ake yi wa hidima don su zama tsanin biyan bu}ata a bautar kan-gida. An yi bayani daki-daki kan yadda ake ro}on bu}atu zuwa ga aljanun da ake yi wa bautar kan-gida. Sannan aka jero sunayen aljanun tare da ire-iren kirarin da ake yi wa kowane aljani a lokacin da ake gudanar da bautar don neman biyan bu}ata. A yi bayanai kan sharu]]an da ake iya samu wajen bautar kowane aljani a matsayin kan-gida. An na]e babin ta hanyar ta}aita bayanan da babin ya }unsa. A babi na biyar kuwa jawabin kammalawa ne, sai manazarta ta biyo bayansa.

1.1 Bitar Ayyukan Da Suka Gabata

Ibrahim (1983) kundin digirin farko (B.A) wanda aka gabatar a jami’ar Usmanu danfodiyo da ke sakkwato. Ya rubuta kundin mai taken Camfe Camfen Hausawa;. A cikin wannan kundin, Awaisu ya yi {okarin kawo bayani a kan camfe- camfen Hauwasa da suka shafi kiyon lafiya da masu ala}a da tsimi da tanadi,siffofin camfi tare da sigoginsu. Sai kuma inda ya ta~o camfi mai ala}a da addinin musulunci, wa]anda dukkanninsu akwai camfecamfe, wa]anda akwai camfi da Bahaushe yake dasu a kan hakan. Duk da yake dai wannan marubucin ya ta~o kan zancen taken bincike da nake son yi dangane da abin daya shafi camfi. Amma kuma har wayau, bai ta~o camfin da akan samu dangane da al’adun Bahaushe ba. wanda yake ni fannin bincikena ya }unshi camfin daya shafi aure, haihuwa da mutuwa.

Abdullahi, (2002) kundin digirin farko(B.A) wanda

aka gabatar a Jami’ar Usmanu danfodiyo da ke sakkwato.Ya rubuta kundin mai taken, kambarin kwantagora. Tarihinsu da Al’adunsu; A cikin wannan kundin, zakariya’u ya yi }okarin bayani a kan matakan rayuwar Bahaushe, wato aure haihuwa da kuma mutuwa. Amma kash! Bai ta~o ire iren camfe – camfen da ake samu a cikin wadannan matakan rayuwa ba. wanda ni nawa

binciken, zai fede biri har wutsiya.

Yaro, (1986) kundin digirin farko (B.A) wanda aka gabatar  a jami’ar Usmanu danfodiyo da ke sakkwato. Ya rubuta kundin mai taken ala}a da bambance-bambancen

Al,adun Hausawa da na }abilar jaba, shima Abubakar ya yi rawar gani dangane da al’adun Hausawa da suka shafi sallar idi, yawon sallah, aure,aski, la}abi. Haka kuma, ya yi Magana dangane da mutuwa zaman makoki . amma har ila yau, bai yi magana a kan camfi ba. da wannan ne naga na }ara samun }arfin guiwa wurin yin bincikena.

Gado, (2007) kundin digirin farko (B.A) wanda aka gabatar  a jami’ar Usmanu danfodiyo da ke sakkwato. Ya rubuta kundin mai taken tarihin tsafe-tsafen kambari da gungawa na magani a kan Hausawa Mazauna yauri. A cikin wannan kundi, Aliyu Gado ya yi bayani dangane da abin daya shafi tsafi. Inda ya yi }o}arin bayyana ma’anarsa tare da yadda tsafe-tsafen kambarin yauri yake. Wanda yake a al’adar Bahaushe akwai tsakanin camfi da tsafi. Domin kuwa yadda matsafa suka  suke amfani da tsafinsu a matsayin addininsu, haka camfi camfi sukan ]auke shi kamar addini a wani fagen. Amma duk da haka, Aliyu bai yi Magana dangane da abin daya Safi tasirin camfi a matakan rayuwar Hausawa ko abin daya shafi hakan ba. wannan ne ya }ara mini }warin guiwa wurin yin nawa

binciken.

Wasagu,  (1999) kundin digirin farko (B.A) wanda aka gabatar a jami’ar Usmanu danfodiyo da ke sakkwato. Ya rubuta kundin mai taken tasirin Aure Hausawa a kan na

Dakarkari Zuru; A cikin wannan kundin, Bashar ya yi

{o}arin bayyani kan ]aya daga cikin matakan rayuwar Bahaushe, wato aure ,amma kash! Bai ta~o ire-iren camfecamfen da ake samu a wannan mataki na rayuwar Bahaushe ba. wanda yake ni kuma nawa kundin, zai fede biri har wutsiya.

Abubakar, (2005) kundin digirin farko (B.A) wanda aka gabatar a jami’ar Usmanu danfodiyo da ke sakkwato. Ya rubuta kundin mai taken Camfi A cikin Akushin Bahaushe ; shima wannan bawan Allah, a cikin kundinsa ya yi {o}arin bayani dangane da abin daya shafi kan zancen binciken, wato camfi. Inda ya yi tsokaci a kan samuwar camfi, yadda Bahaushe yake, ma’anarshi da misalanshi da kuma makamantan haka. Amma shi ma har ila yau, bai yi

Magana akan camfe-camfe da suka shafi matakan rayuwar Bahaushe ba. wato aure, haihuwa da kuma mutuwa.

Abu, (1985) kundin digirin farko (B.A) wanda aka gabatar a jami’ar Usmanu danfodiyo da ke sakkwato. Shi kuwa Ya rubuta kundin mai taken  Al,adun aure a katsina  da canje-canjen da ake samu, a cikin wannan kundin,

Muhammadu abu ya yi {o}arin bayani dangane da abin daya shafi matakan rayuwar Bahaushe, wato aure. Inda ya yi tsokaci kan ma’anar aure da muhimmancinsa. Ya kuma yi bayanin aure kafin zuwan musulunci da kuma nau’oinsa. Wanda yake aure abu ne mai Matu}ar muhimmanci ga rayuwar ]an’adam. Kuma shi ne ginshi}in rayuwar  kowace al’umma. Amma kuma duk da haka, bai yi Magana a kan ire-iren camfe-camfen da suka shafi matakan rayuwar Bahaushe ba. Wani aikin da aka gabatar shin a,

Tsafe, (2010) ya aiwatar das hi kan Maguzawan Tsagero, manazarcin ya kawo bayanai kan al’adun rayuwar Maguzawan Tsagero tun daga tarihin su zuwa yanayin auratayyarsu da bukukuwan da sukan yi a lokutan aure da haihuwa da mutuwarsu. Haka kuma ya kawo bukin cikar shekara da na kaciya. Manazarcin ya kawo ire-iren tsafacetsafacen da Maguzawan kan yi don tsaron kai ko don cuta wa wani. Inda ya waiwayi maganar sammu wanda ya shafi cimaka da na turbu]a da kiranye da harbin kasko da aiken aljanu da na faskara da baduhu da sagau da makantansu. Wannan aikin yana da ala}a da wannan nazarin saboda dukan su a kan Maguzawa ake gudanar das u, sai dais hi wannan a kan Maguzawan Tsagero aka gudanar. Inda shi kuma wannna nazarin za a dubi yadda Maguzawan

Kwatarkwashi ke gudanar da bautarsu wadda ta shafi tsafin

kan-gida.

 

1.2 Dalilin Bincike

Komai na da dalili idan har za a gudanar da shi, don haka wannan nazari yana da nashi dalilin da ya sa aka gudanar da shi. Daga cikin dalilan sun ha]a da:

  • Cika }a’idojin da jami’a ta shimfi]a kan duk wani ]alibi da ya zo shekarar }arshe ta karatu don ya ba da ta shi gudunmuwa a fagen da yake karatu.
  • Na biyu domin bun}asa da kuma ciyar da al’adun Hausawa na gargajiya gaba. Musamman magunguna da suka shafi tsaro a rayuwar al’ummar Hausawa.
  • Lokacin da ake gudanar da bitar ayyukan da suka gabata, ba a ci karo da wani aiki da ya yi daidai da wannan bincike ba, ko ta fuskar take, ko tsarin aiki ko manufa. Don haka wannan aikin ya sami dalilin

gudanuwa.

  • Wani dalilin shi ne ba a ci karo da wani aiki da aka yi a kan-gidan }asar Kwatarkwashi ba.

 

 

1.3 Manufar Bincike

Manufar wannan bincike shi ne fito da irin bautar da al’ummar Maguzawan Kwatarkwashi suke gudanarwa wadda ta shafi addini ta fuskar maganin gargajiya na tsaro, da irin gudummawar da maganin yake bayarwa ga masu amfani da shi bisa imaninsu. Yin haka zai tabbatar wa sauran al’ummu da suke yi wa al’ummar Hausawa kallon bai-]aya ta fuskar addini tabbacin cewa Hausawa musamman ma na }asar Zamfara ba dukkan su ba ne musulmi kamar yadda wasu suke kyautata tunaninsu. Domin tabbatar da hakan da kuma kawar da tunanin masu tunani kan cewa duk Bahaushe musulmi ne shi ya sa

wannan aikin ya yi }o}arin fito da tsarin bautar da ta shafi tsaro na Hausawan da ake kira Maguzawa na }asar Kwatarkwashi

fili.

 

1.4     Farfajiyar Bincike

Wannan bincike  an ke~e masa muhallin gudanar da shi ne a }asar Kwatarkwashi ta jihar Zamfara. Inda aka gudanar da binciken kan batun ire-iren bautar da Hausawa Maguzawa na }asar Kwatarkwashi suke yi domin tsaro ga muhallinsu da zuriyarsu da sana’ar da suke aiwatar wa a }asar Kwatarkwashi, tare da bayyana irin mahimmancinsa. Farfajiyar wannan binciken za ta kasance ne a }asar Kwatarkwashi da ke jihar

Zamfara.

1.5     Hanyoyin Gudanar Da Bincike

Manyan hanyoyin da za a bi wajen gudanar da wannan binciken su ne kamar haka:

  1. za a yi hira da manyan mutane na }asar Kwatarkwashi maza da mata wa]anda suka san abin da ake kira kangida.
  2. Za a gudanar da karance-karance na litattafan tarihi da suka shafi }asar Kwatarkwashi da al’ummar }asar domin samun nasarar kammaluwar wannan binciken.
  3. Ziyartar ]akunan karatu na manyan makarantu zai

taimaka wajen tattaro bayann da suka dace da wannan binciken.

  1. Duba mujallu da }asidu da mu}alu da aka buga, hanya ce babba da za a inganta wannan nazarin binciken.
  2. Za a dubi mahimman ayyukan da aka gudanar a fagen ilimi, wato kamar ire-iren kundayen da manazarta suka gudanar a

jami’o’i.

 

1.6     Muhimmancin Bincike

Bincike kowane iri ne yana da muhimmanci ga rayuwar al’umma, da yake zai iya ilmantarwa a kan wani abu da  ba a sani ba, ko ya fito da muhimmancin wani abu don mutane su yi koyi don su amfana. Ko kuma ya fito da illar wani abu don mutane su guje masa. Saboda haka shi ma wannan bincike yana da nasa muhimmanci.

Wannan binciken ya shafi ]aya daga cikin hanyoyin bautar gargajiya da ta shafi magani don tsaro wanda ake aiwatarwa a garin Kwatarkwashi. Saboda haka zai zama a matsayin cike gurbi ne a kan abin da aka bari a baya wajen bayyana jerin hanyoyin bautar gargajiya ta al’ummar Hausawa. Wannan nazari zai taimaka wa ]alibai ta fuskar samun damar sanin irin yadda ake gudanar da bautar gargajiya a }asar Hausa, musamman wadda  ta shafi tsaro don wajen dogaro da kai da taimakawa wajen hana munan al’adu a }asar Hausa.

Kammala wannan bincike zai fito da tsarin bautar kangida fili don nuna wa duniya cewa Hausawa basu bauta wa gumaka ba a lokacin jahiliya, aljanu suka bauta wa don neman biyan bu}atunsu na rayuwa. kundin zai taimakawa sauran ]alibai  suma, su mayar da hankali wurin bincike a kan irin wa]annan nazarce-nazarce da suka karanta musamman irin tsofaffin al’adun gargajiya da suke taimakawa wajen bayar da ingantacciyar rayuwar al’umma.

1.7 Na]ewa

Bayan shimfi]a ga ba}o in ya tafi sai a na]e. Don haka a nan za a na]e wannan babin da ta}aitaccen bayanin abin da babin ya }umsa. Abin lura a nan shi ne, duk  ayyukan da aka gudanar  wajen bitar aikin da suka gabaci wannan aikin, ba a sami wani aiki da ya yi dai dai ko kamanci da aikin ba, ko da ta fuskar  take. Don haka aka fito da bayani a fili  na cancantar gudanar da wannan aikin da aka aiwatar, don samun damar gudanar da wannan bincike. {udirin wannan aiki shi ne samar da

}wa}}waran aiki wanda zai yi matu}ar tasiri ga rayuwar Hausawa da ma wa]anda ba Hausawa ba. Domin fito da tsarin bautar Hausawa fili saboda sauran jama’a da suke yi wa Hausawa kallon masu bautar gumaka a zamanin jahiliya su bari kuma su san cewa imanin Bahaushe a gargajiyance shi ne na bauta wa iskoki.

TSAFI KO MAGANI: TA{AITACCEN NAZARIN KANGIDA DA NAU’O’INSA A {ASAR KWATARKWASHI 

Leave a Reply